Manchester City ta kammala sayen Bony

Wilfred Bony Hakkin mallakar hoto manchester city
Image caption Bony zai wakilci Ivory Coast a gasar cin kofin nahiyar Afirka

Manchester City ta kammala sayen dan wasan Swansea City, Wilfried Bony, kan kudi fam miliyan 28.

Bony ya amince da yarjejeniyar kwantiragin shekaru hudu domin ya taka leda a Ettihad, kuma zai saka riga mai lamba 14.

Bony ya koma Swansea ne kan kudi fam miliyan 12 daga Vitesse Arnhem a shekarar 2013, kuma shi ne kan gaba wajen zura kwallaye a raga a gasar Premier a shekarar 2014 inda ya ci kwallaye 20.

Kungiyoyin biyu sun cimma yarjejeniya ne a karshen makon jiya, kuma City za ta biya fam miliyan 25 nan take da kuma karin fam miliyan uku nan gaba idan dan wasa ya yi kwazo a wasanninsa.

Sayen Bony da City ta yi yasa dan kwallon ya zamo daya daga cikin 'yan wasan Afirka da suka fi daukar albashi a tarihi.

Dan wasan yana cikin tawagar kwallon kafar Ivory Coast da zai buga mata gasar cin kofin nahiyar Afirka a Equatorial Guinea, kuma sai bayan gasar ne zai fara buga wa City kwallo.