Arteta da Debuchy za su yi jinyar watanni 3

Arteta Debuchy Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan biyu suna fama da jinyar rauni a bana

'Yan kwallon Arsenal Mikel Arteta da Mathieu Debuchy za su yi jinyar watanni uku, bayan da likitoci suka yi musu tiyata.

Arteta mai shekaru 32, an cire masa wani kashi ne a kafarsa ta hagu, wanda yake hana dan kwallon sakewa a watannin baya.

Shi kuwa Debuchy da bai dade da dawowa daga jinya ba, an yi masa aiki ne a kafada a raunin da ya ji lokacin da suka kara da Stoke City a gasar Premier.

Wasanni 14 Dabuchy ya buga wa Arsenal, tun lokacin da ya koma kulob din daga Newcastle kan kudi fam miliyan 12 a watan Yulin bara.

Ranar Asabar Arsenal za ta kara da Manchester City a gasar Premier, watakila tsakanin Kieran Gibbs ko Hector Bellerin ko kuma Calum Chambers wani ya maye gurbinsa.