Mai yiwuwa Fletcher zai bar Man U.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fletcher ya yi nasara

Mai yiwuwa dan wasan Manchester United, Darren Fletcher, zai bar kulob din a lokacin musayar 'yan wasa.

Kulob-kulob da dama suna sha'awar daukar dan wasan bayan ya samu nasarori da yawa.

An bai wa dan wasan tsakiyar mai shekaru 30 mukamin mataimakin kyaftin lokacin da kociya, Louis van Gaal, ya karbi ragamar kulob sai dai kwantaraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta bana.

Rahotanni na cewa kociyan West Brom Tony Pulis na cikin wadanda ke son daukar Fletcher.

Dan wasan ya buga wasanni ukun farko a kakar wasa ta bana, kuma babu atisayen da ba a yi da shi ba.