Wanyama zai yi jinyar mako biyar

Image caption Da ma dai Wanyama yana fama da wasu raunukan

Kociyan Southampton Ronald Koeman ya ce yana jin tsoron cewa dan wasan kulob din Victor Wanyama ka iya yin jinyar makonni biyar bayan raunin da ya yi a kafadarsa.

An fitar da dan wasan daga fili gabanin su tafi hutun rabin lokaci a wasan da suka doke Ipswich da ci 1-0 a Gasar cin Kofin FA.

Da ma dai kociya Koeman yana so ne Wanyama ya buga wasa na mintuna arba'in da biyar.

Ya ce, "da ma yana fama da wasu raunukan; idan dai kafadarsa ce ta goce to da alama zai yi jinyar makonni hudu ko biyar."

Hakan dai zai sa Wanyama ba zai buga karawar da kulob din zai yi da Liverpool ba ranar 22 ga watan Fabrairu, da kuma wadda za su yi da Newcastle, Swansea, Queens Park Rangers da kuma West Ham.

Wanyama na daya daga cikin 'yan wasa masu kwazo a Southampton, saboda ya buga wasa a dukkanin fafata wa 24 da kulob din ya yi.