Rukunin A

Hakkin mallakar hoto GETTY

Kasashe 16 ne za su fafata a gasar cin kofin nahiyar Afirka na bana da Equatorial Guinea za ta karbi bakunci, wanda za a kara a wasanni 32 cikin kwanaki 18 domin fitar da zakaran bana.

Tun farko sai kasashen sun samu damar fitowa daga cikin rukunin da suke, wanda kowanne ya kunshi tawagar kasashe hudu, kuma wadda ta kare a matsayi na daya da kuma na biyu ne za su buga wasannin zagayen gaba.

Sashin wasanni na BBC ya yi bincike kan yadda za a kara a gasar, ya kuma zakulo muku manyan batutuwa da suka shafi kasashen.

Rukunin farko: Burkina Faso da Congo da Equatorial Guineada kuma Gabon

Equatorial Guinea

 • Ta halarci gasar sau: 1
 • Kwazon da ta fi yi: Kai wa wasan daf da na kusa da karshe (2012)
 • Kociyanta: Esteban Becker (Argentina)
 • Fitatcen dan kwallonta: Emilio Nsue
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 120.

Equatorial Guinea ta samu gurbi a gasar cin kofin nahiyar Afirka ne bayan data maye gurbin Morocco--tun a farko an kore ta daga buga wasannin neman tikitin shiga gasar sakamakon samun ta da aka yi da yin amfani da dan wasan da ya karya ka'ida. Ita ce kasar da take wajen mataki na 100 a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya a gasar, kuma ta nada kociyanta Becker saura kwanaki 11 a fara buga gasar.

Burkina Faso

 • Ta halarci gasar sau: 9
 • Kwazon da ta fi yi: Kai wa wasan karshe (2013)
 • Kociyanta: Paul Put (Belgium)
 • Fitattun 'yan kwallonta: Alain Traore da Jonathan Pitroipa
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 63.

Burkina Faso ta bai wa kowa mamaki da ta kai wasan karshe a gasar da Afirka ta kKudu ta karbi bakunci. Kuma daya da nema Nigeria ta doke ta a karawar. Tawagar Stallion bata taba lashe wasa a wata kasarsa daga cikin wasanni 21 da ta buga. Dan wasanta Pitroipa ne ya zamo fitatcen dan kwallo a gasar da aka kammala a shekarar 2013-- kuma ya zura kwallaye 6 a wasannin neman shiga gasar bana.

Gabon

 • Ta halarci gasar sau: 5
 • Kwazon da ta fi yi: Kai wa wasan daf da na kusa da karshe (1996 da 2012)
 • Kociyanta: Jorge Costa (Portugal)
 • Fitaccen dan kwallonta: Pierre-Emerick Aubameyang
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 65.

Tawagar kwallon kafar Gabon daya ce daga cikin kasashe hudun da ba'a doke su ba a wasannin neman tikitin shiga gasar bana da suka hada da Afirka ta Kudu da Kamaru da kuma Tunisia. Wasa daya kacal suka lashe a gasar 1996 lokacin da suka samu nasara akan Zaire wadda yanzu ake kira DR Congo. Gabon ta yi hadakar karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka tare da Equatorial Guinea a shekarar 2012.

Congo

 • Ta halarci gasar sau: 6
 • Kwazon da ta fi yi: Lashe kofin a shekarar (1972)
 • Kociyanta: Claude LeRoy (France)
 • Fitaccen dan kwallonta: Prince Oniangue
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 61.

Rabon da Congo ta halarci gasar cin kofin nahiyar Afirka tun a shekarar 2000. Kociyanta Claude LeRoy ya lashe kofin tare da Kamaru a shekarar 1988 kuma wannan ne gasar wasanni na takwas da kocin ke halarta a tarihance. Kuma tawagar kwallon Congo ce ta yi waje da Nigeria mai rike da kofin shekarar 2013 daga shiga gasar bana.