Rukunin B

Hakkin mallakar hoto

Rukuni na biyu B: Zambia da DR Congo da Tunisia da kuma Cape Verde

Zambia

 • Ta halarci gasar sau: 16
 • Kwazon da ta fi yi: Lashe kofin (2012)
 • Kociyanta: Honour Janza (Zambia)
 • Fitattun 'yan kwallonta: Rainford Kalaba da Kennedy Mweene da kuma Stopilla Sunzu
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 46.

Zambia ce ta lashe kofin Afirka a shekarar 2012 a lokacin da hadar Equatorial Guinea da Gabon suka karbi bakunci. Sai dai kasar ta kasa kare kambunta shekara daya tsakani a inda aka fitar da ita a gasar ba tare da ta ci wasa ko guda daya ba, kuma tawagar kasar har yanzu tana da 'yan 10 da suka lashe gasar a shekarar 2012.

DR Congo

 • Ta halarci gasar sau: 16
 • Kwazon da ta fi yi: Ta lashe kofin a shekarar (1968, 1974)
 • Kociyanta: Florent Ibenge (DR Congo)
 • Fitattun 'yan kwallonta: Yannick Bolasie da Dieumerci Mbokani
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 56.

Kasar DR Congo bata sake kai wa wasan daf da na kusa da karshe tun daga shekarar 2006. Kuma kociyanta Ibenga ya hada tawagar 'yan wasansa ne da 'yan kwallon kulob din AS Vita wadda ta zamo ta biyu a gasar cin kofin zakarun Afirka. Har yanzu dan wasan DR Congo ne ke rike da tarihin dan kwallon da ya fi zura kwallo a gasa guda a tarihin gasar, a inda ya ci kwallaye tara a shekarar 1974.

Tunisia

 • Ta halarci gasar sau: 16
 • Kwazon da ta fi yi: Lashe kofin a shekarar (2012)
 • Kociyanta: George Leekens (Belgium)
 • Fitattun 'yan kwallonta: Youssef Msakni da kuma Fakhreddine Ben Youssef
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 22.

Wannan ne karo na 12 da Tunisia ke halartar gasar cin kofin nahiyar Afirka a jere--tarihin da babu kasar da ta kafa shi. Sai dai kuma sau daya ta dauki kofin a lokacin data karbi bakunci a shekarar 2004, a inda ta doke abokiyar hamayyarta Morocco a wasan karshe. Tunisia ta kai wasan daf da na kusa da karshe karo hudu daga cikin gasa shida baya amma anyi waje da ita a wasannin cikin rukuni a shekarar 2013.

Cape Verde

 • Ta halarci gasar sau: 1
 • Kwazon da ta fi yi: wasan daf da na kusa da karshe (2012)
 • Kociyanta: Rui Aguas (Portugal)
 • Fitattun 'yan kwallonta: Babanco da Heldon da kuma Mendes
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 40.

Cape Verde ce karamar kasar da ta fara halartar gasar cin kofin Afirka a shekarar 2013, kuma duk da halartar gasar a karon farko da ta yi sai da ta kai wasan daf da na kusa da karshe. Dukkan tawagar 'yan wasan kasar suna taka leda ne a wajen kasar.