Rukunin C

Rukuni na uku: Senegal da Afirka ta Kudu da Ghana da kuma Algeria

Ghana

 • Ta halarci gasar sau: 19
 • Kwazon da ta fi yi: Lashe kofin a shekarun (1963, 1965, 1978, 1982)
 • Kociyanta: Avram Grant (Israel)
 • Fitattun 'yan kwallonta: Asamoah Gyan da Andre Ayew
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 37.

Ghana ta kai wasan kusa da na karshe sau hudu a jere a baya. Black Stars wadda ta lashe kofin karo hudu ta dade bata dauki kofin ba da ya kai shekaru 33 rabonta da shi, kuma Tsohon kociyan Chelsea Grant ne ya karmi ragamar horar da su a watan jiya.

Algeria

 • Ta halarci gasar sau: 15
 • Kwazon da ta fi yi: Lashe kofin a shekarar (1990)
 • Kociyanta: Christian Gourcuff (France)
 • Fitattun 'yan kwallonta: Yacine Brahimi da Sofiane Feghouli da kuma Islam Slimani
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 18.

An fitar da Algeria a wasannin cikin rukuni a shekarar 2013, sai dai tun daga lokacin kasar ta dare mataki na daya a jerin kassshen da suka fi iya murja leda a Afirka, sannan ta kai matsayin wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil a karon farko a shekarar 2014. Dan kwallon kafar kasar ne Yacine Brahimi ke rike da kambun gwarzon dan wasan kwallon kafar Afirka da ya fi yin fice da BBC ta karrama.

Afirka ta Kudu

 • Ta halarci gasar sau: 8
 • Kwazon da ta fi yi: Lashe kofin a shekarar (1996)
 • Kociyanta: Ephraim 'Sakes' Mashaba (Afrika ta Kudu)
 • Fitattun 'yan kwallonta: Dean Furman da kuma Tokelo Rantie
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 52.

Afirka ta Kudu ta lashe kofin a karon farko data shiga gasar a shekarar 1996. Kuma tawagar 'yan wasan kasar suna fatan za su lashe kofin bana domin karrama kyaftin dinsu koma gola Senzo Meyiwa wanda aka harbe har lahira a watan Disambar Bara. Wasa daya Bafafa Bafafa ta lashe daga cikin wasanni 12 data buga a baya a gasar.

Senegal

 • Ta halarci gasar sau: 12
 • Kwazon da ta fi yi: Zama ta biyu a shekarar (2002)
 • Kociyanta: Alain Giresse (France)
 • Fitattun 'yan kwallonta: Mohamed Diame da Papiss Cisse da kuma Mame Biram Diouf
 • Matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka leda na FIFA: 35.

Tarihin Senegal a gasar a baya ba wani abin tunkaho bane--wasa daya suka lashe daga cikin karawa tara da suka yi a baya. Nasarar da suka samu ita ce wadda suka doke Guinea a shekarar 2006 a wasan daf da na kusa da karshe, sai dai kuma kwallo daya ce ta shiga ragarsu a wasannin neman tikitin shiga gasar bana.