Eq Guinea da Congo sun tashi kunnen doki

Emilio Nsue
Image caption Ranar Laraba Equatorial Guinea za ta kara da Burkina Faso

Mai masaukin bakin gasar cin kofin nahiyar Afirka Equatorial Guinea, ta tashi wasa kunnen doki da Congo a wasan farko cikin rukunin farko a filin wasa na Bata.

Equatorial Guinea ce ta fara zura kwallo a minti na 16 da fara tamaula ta hannun dan wasanta Emilio Nsue.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Congo ta farke kwallonta ta hannun Thievy Bifouma saura minti uku a tashi daga wasan.

Za'a fafata a wasa na biyu a cikin rukunin farkon tsakanin Equatorial Guinea da Burkina Faso da kuma karawa tsakanin Gabon da Congo ranar Laraba.