Gabon ta doke Senegal da ci 2-0

Pierre-Emerick Aubameyang Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gabon za ta kara da Congo ne ranar Laraba

Gabon ta fara gasar cin kofin nahiyar Afirka da kafar dama, bayan da ta doke Senegal da ci 2-0 a karawar da suka yi a wasan rukunin farko wasa na biyu ranar Asabar.

Pierre-Emerick Aubameyang ne ya fara zura kwallon farko a minti na 19 da fara tamaula, yayin da Malick Evouna ya kara ta biyu saura minti takwas a tashi daga wasan.

Gabon ta dare matsayi na daya kenan a cikin rukunin da maki uku, sai Equatorial Guinea da Congo da suke da maki daya kowannensu da kuma Senegal a matsayi na karshe.

Za'a ci gaba da wasannin rukunin farko tsakanin Equatorial Guinea da Burkina Faso sannan karawa tsakanin Gabon da Congo ya biyo baya ranar Laraba.