Gyan na fama da zazzabin cizon sauro

Asamoah Gyan Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Ghana tana rukuni na uku tare da Senegal da Algeria da Afirka ta Kudu

Watakila kyaftin din tawagar kwallon kafar Ghana, Asamoah Gyan, ba zai buga karawar da za su yi da Senegal a gasar kofin Afirka ba ranar Litinin.

Kyaftin din bai samu yin atisaye da 'yan wasa ba kwanaki biyu da suka wuce sakamakon kamuwa da ya yi da zazzabin cizon sauro.

Tun a ranar Asabar da dare aka kai Gyan asibitin Mongomo, amma an sallamo shi da sanyin safiyar Lahadi.

Likitoci na duba yuwuwar ko dan wasan zai iya murmurewa kafin wasan da za su buga da Senegal na rukuni na uku a Mongomo ranar Litinin.