Arsenal ta doke Man City 2-0 har gida

Mancity Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal ta koma matsayi na biyar a teburin Premier

Arsenal ta doke Manchester City da ci 2-0 a Ettihad a gasar Premier wasan mako na 22 da suka kara ranar Lahadi.

Arsenal ta fara zura kwallo ne a bugun fenarity da Cazorla ya ci a minti na 24 da fara tamaula, kafin Giroud ya kara ta biyu a minti na 67.

Yanzu tazarar maki biyar ne tsakanin Manchester City wacce ke matsayi na biyu a teburin Premier da Chelsea mai matsayi ta daya wadda ta doke Swansea 5-0 ranar Asabar.

Da wannan sakamakon Arsenal ta koma matsayi na biyar a teburin Premier da maki 39.