'Ba dole sai mun dauko mai tsaron baya ba'

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana mataki na biyar a teburin Premier da maki 39

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce ganganci ne idan ba su dauko mai tsaron baya ba a cikin watannan, amma ba dole ba ne sai sun dauko.

Arsenal tana fama da karancin masu tsaron baya sakamakon yawan jinya da 'yan wasanta ke yi, kamar Laurent Koscielny da Kieran Gibbs da Nacho Monreal da kuma Mathieu Debuchy.

Wenger ya ce ganganci ne su ki kara dauko mai tsaron baya a bana, domin duk lokacin da mai tsaron baya daya ko biyu suka ji rauni sai mun shiga matsi.

Debuchy zai yi jinyar watanni uku bayan da aka yi masa aiki a kafadarsa ta hagu, kuma saura masu tsaron baya shida masu lafiya kenan suka rage wa Arsenal.