Real Madrid ta doke Getafe da ci 3-0

Getafe Madrid Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Har yanzu Madrid tana matsayi na daya a teburi da maki 45

Real Madrid ta doke Getafe har gida da ci 3-0 a gasar La Liga, wasan mako na 18 da suka fafata ranar Lahadi.

Ronaldo wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da ya fi yin fice ne a 2014 ne ya zura kwallaye biyu, sannan Gareth Bale ya kara ta uku.

Madrid tana matakinta na daya a kan teburin La Liga da maki 45, bayan da ta buga wasanni 18.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Real Sociedad ranar Asabar 31 ga watan Janairun 2015.