Messi ya ci wa Barca kwallaye uku a wasa sau 30

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Barcelona tana matsayi na biyu a teburin La Liga da maki 44

Lionel Messi ya ci wa Barcelona kwallaye uku a wasa sau 30 a karawar da suka doke Deportivo La Coruna da ci 4-0 har gida a gasar La Liga a ranar Lahadi.

Messi wanda ya gaza lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa da ya fi yin fice a shekarar 2014, ya fara zura kwallo a raga a minti na 10 da fara wasan.

Dan wasan ya kara ta biyu ne lokacin da ya karbi kwallo daga wajen Neymar ya kuma buga ta wuce golan Deportivo Fabricio Agosto ta fada raga.

Messin ya ci kwallo na uku kuma na 30 da ya ci wa Barcelona a wasanni a minti na 62, kafin Da Silva Junior ya ci gida kwallo na hudu.

Yanzu haka Messi ya zura kwallaye shida a raga a cikin wasanni takwas da suka wuce kuma nasara ta 14 da Barcelona ta samu daga cikin wasanni 19 da ta buga a gasar La Liga.