Ana daukar matakai kan Ebola a kofin Afirka

Ebola risk
Image caption Equatorial Guinea ce ta maye gurbin Morocco wacce ta ki karbar bakuncin saboda Ebola

Hukumomi a Equatorial Guinea suna daukar matakan kaucewa yada cutar Ebola a filayen da ake gudanar da gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Shugaban hukumar kwallon kafar kasar ne Andres Jorge Mbombio ya sanar da hakan, a inda ya ce sai an gwada mutum sannan ya wanke hannuwansa kafin ya shiga kallon wasa.

'Yan sanda da magoya baya sun yi taho mu gama a karawar da aka yi tsakanin Zambia da Jamhuriyar Congo, sakamakon dogon layi da aka yi kafin 'yan kallo su samu shiga filin wasa.

Equatorial Guinea ce ta maye gurbin Morocco wacce ta bukaci hukumar kwallon kafar Afirka ta dage gasar sakamakon tsoron kamuwa da cutar Ebola.