Kofin Afirka 2015: Senegal ta doke Ghana 2-1

Ghana Senegal Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ghana za ta kara da Algeria, Senegal da Afirka ta Kudu ranar Juma'a

Tawagar kwallon kafar Senegal ta doke Ghana da ci 2-1 a gasar cin kofin nahiyar Afirka a wasan farko a rukuni na uku a filin Mongomo.

Ghana ce ta fara zura kwallo a bugun fenariti da Andrew Ayew ya ci a minti na 14, kafin Dioup ya farke kwallo bayan an dawo daga hutu, kuma Sow ya kara ta biyu daf da tashi daga wasan.

Kyaftin din Ghana Asamoah Gyan bai buga karawar ba, sakamakon kamuwa da ya yi da zazzabin cizon sauro.

Ghana za ta kara da Algeria a wasa na biyu daga cikin rukunin, daga baya a fafata tsakanin Senegal da Afirka ta Kudu ranar Juma'a.