Dole mu kara zage-dantse - Enrique

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luis Enrique ya ce dole su kara zage-dantse

Kociyan Barcelona Luis Enrique ya ce dole kulob din ya kara zage-dantse idan suna son daukar Kofin Gasar La Liga ta Spaniya.

Barca na bayan jagorar gasar, Real Madrid da maki daya, bayan Lionel Messi ya zura kwallaye uku shi kadai a wasan da suka doke Deportivo La Coruna da ci 4-0.

Kungiyar -- wacce ta zo ta biyu a kakar wasan da ta wuce -- kawo yanzu ta kasa koma wa kan ganiyarta, duk da cewar kwallaye tara kacal aka zura mata cikin wasanni 19 a gasar La Liga.

Enrique ya ce, "akwai abubuwan da suka kamata mu kara kaimi a kansu, a bangaren kai hare-hare da kuma tsaron gida. Wannan ce kawai hanyar da za mu iya lashe gasar."