Redknapp zai ci gaba da zama a QPR - Fernandes

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption QPR dai shi ne na biyun karshe a tebirin Gasar Premier

Shugaban hadakar kulob-kulob da ke gasar Premier, Tony Fernandes , ya ce kociyan QPR, Harry Redknapp zai ci gaba da zama kan mukaminsa.

Kulob din dai shi ne na biyu a kasan tebirin gasar, lamarin da ya sa ake ganin Redknapp na fuskantar barazanar ajiye mukamin nasa.

Sai dai wata sanarwa da Fernandes ya wallafa a shafin intanet, ya ce "Ina gani lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan jita-jita domin kowa ya mayar da hankali kan abin da yake gabansa".

Ya kara da cewa ya yi amanna Harry ne mutumin da ya fi dacewa ya fitar da kulob din daga halin da yake ciki.

Wasu labarai da suka fito a makon jiya sun bayyana cewa za a kori Redknapp daga mukaminsa bayan sun sha kashi a hannun Manchester United da ci 2-0 a wasan da suka yi.

Bayan wasan ne Redknapp ya dora alhakin kayen da suka sha kan "wasu mutane da ke son ganin bayan kulob din".