Sampdoria na daf da dauko Samuel Eto'o

Samuel Etoo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Eto'o ya yi ritayar buga wa Kamaru tamaula

Kulob din Sampdoria na Italiya na fatan kammala dauko dan wasan Everton Samuel Eto'o zuwa ranar Talata.

Dan kwallon Kamarun mai shekaru 33, ya koma Everton ne kan yarjejeniyar kwantiragin shekaru biyu a watan Agusta, a inda ya zura kwallaye hudu daga wasanni 20 da ya buga mata.

Sampdoria na kokarin samun gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da take matsayi na hudu da maki daya da Napoli a kan teburin Serie A.

Eto'o ya fara murza leda a Real Madrid, amma ya fi yin fice a Barcelona daga nan ya koma Inter Milan da Chelsea da kuma Anzhi Makhachkala.