Kofin Afirka 2015: Za mu doke Gabon - Malonga

Dominique Malonga Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Congo za ta kara ne da Gabon ranar Laraba

Dan kwallon tawagar Congo, Dominique Malonga, ya ce za su zage damtse su doke Gabon a wasan da za su kara ranar Laraba a gasar kofin Afirka.

Congo sun tashi wasa kunnen-doki da mai masaukin baki Equatorial Guinea a inda Gabon ta doke Burkina Faso a karawar da suka yi ranar Lahadi.

Da wannan sakamakon Gabon ce ke jagaba a rukunin farkon da maki uku, sai mai masaukin baki Equatorial Guinea da Congo da kowannensu ke da maki daya, sannan Senegal da bata da maki.

Malonga ya ce suna sane da cewar Gabon ba kanwar lasa ba ce, saboda haka sun fara shirin hanyoyin da ya kamata su bi domin su doke su.

A rukunin farkon za a kara a wasanni na biyu ne a gasar tsakanin Burkina Faso da Equatorial Guinea, sannan a fafata a wasa na biyu tsakanin Congo da Gabon ranar Laraba.