Liverpool da Chelsea sun tashi 1-1

Liverpool Chelsea Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Chelsea za ta karbi bakuncin Liverpool a wasa na biyu ranar Talata

Kulob din Liverpool ya tashi wasa kunnen doki a gida a gasar Capital One Cup wasan daf da na karshe da suka kara ranar Talata.

Chelsea ce ta fara zura kwallo a bugun fenariti, bayan da Emre Can ya yiwa Hazard keta, kuma dan wasan Belgium din ya buga ya kuma ci kwallon.

Liverpool ta farke kwallonta ta hannun Raheem Sterling a minti na 59, kuma Gerrard ya kusa kara kwallo na biyu, bayan da ya buga ta doki turke.

Liverpool za ta ziyarci Chelsea a karawa ta biyu wasan daf da na karshe na cin Capital One Cup a Stamford Bridge ranar Talata.