Gervinho ya nemi afuwa kan jan kati

Gervinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ivory cost sun tashi wasa da Guinea kunnen doki

Dan kwallon Ivory Coast, Genvinho, ya nemi afuwa bisa jan kati da aka ba shi a ketar da ya yi wa Naby Keita na Guinea a karawar da suka tashi 1-1 ranar Talata.

Dan wasan ya rubuta a shafinsa na sada zumunta na Twitter cewar "Ina neman afuwa daga wajen 'yan kasa da 'yan tawagarmu da magoya baya da mahukuntan gasar bisa laifin da na aikata aka kore ni.

Idan aka bai wa dan wasa jan kati ba zai buga wasa daya ba, amma hukumar kwallon kafar Afirka za ta iya tsawaita yawan wasan da ba zai buga ba a gasar.

Bisa doka idan dan wasa ya yi keta da gangan da kuma ganganci aka sallame shi a wasa, kwamiti zai iya zama ya yanke hukuncin da yake ganin ya fi dacewa.