Attajirin China ya sayi hannun jari a Atletico

Wang Jianlin Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Wang Jianlin na sayen karin kadarori da dama

Attajirin kasar China, Wang Jianlin, ya sayi kaso 20 cikin dari na hannun jarin kulob din Atletico Madrid da ya kai fam miliyan 34.

Jianlin wanda yake shugabantar kamfanin gine-gine da sayar da gidaje mai suna Dalian Wanda, ya sayi kadarori da dama a cikin makon nan.

Cikin kadarorin da ya saya har da gidan sinima na Amurka AMC da kuma wani fitatcen jirgin ruwa na alfarma na Burtaniya mai suna Sunseeker.

Jarin da Jianlin ya zuba a kulob din Atletico ya sa ya zamo dan kasar China na farko da ya zuba hannun jari a daya daga cikin fitattun kungiyoyin nahiyar Turai.

Ya kuma ce hakan zai sa kulob din ya dunga daukar 'yan kwallon China yana buga masa tamaula, wanda hakan zai bunkasa tawagar kwallon kafar China.