Alkalan wasa a Nigeria za su je karo ilimi

Referees Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ne karo na biyu da alkalan za su je horon

Kashi na biyu na tawagar alkalan wasan kwallon kafar Nigeria, za su ziyarci Burtaniya domin karo horo kan sana'arsu ranar Litinin.

Tuni alkalan wasan su 20 suka samu takardun izinin shiga Burtaniya tare da rakiyar shugaban kwamitin alkalan NFF Alhaji Yusuf Ahmed Fresh da kuma shugaban alkalan wasan kwallon kafa na kasar Alhaji Ahmed Maude.

Daga cikin tawagar alkalan da za su samu horon sun hada da mata uku a cikinsu, wanda ake sa ran za su dawo Nigeria ranar 4 ga watan Fabrairu.

Kaso na uku na tawagar alkalan wasan tamaula za su samu damar na su sanin makamar aikin ne a Burtaniya a watan Afirilu mai zuwa.

Ga jerin sunayen alakalan wasan kwallon kafar da aka zabo:

Hadiza Musa, Paul Umuago, Jelili Ogunmuyiwa, Ibrahim Umar Fagge, Jeremiah Akure, Francis Agbaegbu, Mohammed Ahmed Rufai, Bosede Momoh, Ishiaku Ibrahim, Iheanacho Chukwuemeka, Dele Atoun, Abdulrahman Suleiman Jimeta, Uloma Nwogu, Abubakar Audu, Obieze Okiridu, Ezenwankor Obiora, Sunny Atu, Sani Mohammed, Jibrin Isah da kuma Mohammed Aliyu Jingi.