Tunisia ta doke Zambia da ci 2-1

Zambia Tunisia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tunisia za ta kara da Jamhuriyar Congo sai Cape Verde da Zambia ranar Litinin

Tunisia ta doke Zambia da ci 2-1 a gasar cin kofin nahiyar Afirka wasanni na biyu a rukuni na biyu a filin Ebebiyin ranar Alhamis.

Zambia ce ta fara zura kwallo ta hannun Mayuka a minti na 59, daga baya Tunisia ta farke kwallo ta hannun Akaici, sannan ta kara ta biyu ta hannun Chikhaoui saura minti biyu a tashi daga wasan.

Da wannan sakamakon Tunisia tana da maki shida bayan buga wasanni biyu, yayin da Zambia ke da maki daya kacal a wasanni biyun da ta buga.

Tunisia za ta buga wasan karshe na rukunin da Jamhuriyar Congo, a inda Zambia za ta fafata da Cape Verde ranar Litinin.