'Arsenal na tattaunawa kan dauko Paulista'

Gabriel Paulista Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Arsenal ta dauko mai tsaron baya Bielik a makon nan

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce kulob din yana tattaunawa domin ganin ya dauko mai tsaron bayan Villareal Gabriel Paulista.

Wenger ya kara da cewar sun yi nisa akan shirye-shiryen dauko dan wasan, sai dai ya ce ba shi da tabbacin idan za su cimma matsaya, amma yana fatan ya dauko shi.

Arsenal din tana da damar sama wa dan kwallon mai shekaru 24 takardun izinin buga tamaula a Ingila akan lokaci.

A wannan makon ne Arsenal ta dauko Krystian Bielik, mai shekaru 17, daga Legia Warsaw kan kudi sama da fam miliyan 2.

Wenger ya ce Bielik wanda ke tsaron baya daga tsakiya, zai kuma iya amfani da shi a matsayin mai tsaron baya da kuma tsakiya.