Afcon 2015: Eq. Guinea ta kai wasan gaba

Equatorial Guinea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jamhuriyar Congo da Equatorial Guinea ne suka kai wasan daf da na kusa da karshe

Equatorial Guinea ta kai wasan zagaye daf da na kusa da karshe, bayan da ta doke Gabon da ci 2-0 a gasar kofin nahiyar Afirka da suke karbar bakunci.

Balboa ne ya ci kwallon farko a bugun fenariti a minti 10 da dawo wa daga hutu, sannan wanda ya shiga karawar daga baya EdĂș ya kara ta biyu saura minti hudu a tashi daga wasan.

Jamhuriyar Congo ce ta jagoranci rukunin farkon da maki bakwai bayan da ta doke Burkina Faso da ci 2-1.

Equatorial Guinea ta maye gurbin Morocco wacce ta ki karbar bakuncin gasar, sakamakon tsoron kamuwa da cutar Ebola, a inda ta bukaci CAF ta dage gasar.