Villareal da Arsenal sun daidaita kan Paulista

Paulista Hakkin mallakar hoto z
Image caption Arsenal tana mataki na biyar a teburin Premier

Kulob din Villareal ya amince ya bai wa Arsenal aron mai tsaron bayansa Gabriel Paulista, inda shi kuma zai karbi Joel Campbell.

Villareal ne ya bayar da sanarwar a shafinsa na intanet, da cewar ya amince da yarjejeniyar da suka kulla da Arsenal, sannan za a ba shi kudi fam miliyan 15.

Haka kuma kulob din ya sanar da cewar Campbell mai shekaru 22 zai koma wasa a Spaniya har tsawon karshen kakar bana.

Yanzu abun da ya rage a yarjejeniyar shi ne Arsenal ya samar wa da Paulista dan wasan Brazil takardun buga tamaula a Ingila kafin su rattaba hannu kan kwantiragin.