Balotelli baya kan ganiyarsa — Rodgers

Mario Balotelli Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool za ta ziyarci Chelsea wasa na biyu a Capital One Cup ranar Talata

Kociyan Liverpool, Brendan Rodgers, ya ce Mario Balotelli baya kan ganiyarsa a lokacin atisaye, balantana ya buga mana wasa.

Dan wasan mai shekaru 24, har yanzu bai zura kwallo ba a gasar Premier, tun lokacin da aka dauko shi daga AC Milan kan kudi fam miliyan 16 a farkon kakar wasan bana.

Rodgers ya ce "Dan wasan ya fi kowa sanin kwazon da ya kamata ya nuna a lokacin atisaye da zai sa a zabo shi ya taka mana leda a wasa".

Haka kuma kociyan ya ce Daniel Sturridge, zai dawo buga wasa a karawar da za su yi da West Ham a gasar Premier wasan mako na 24 ranar Asabar.

Dan wasan, mai shekaru 25, wanda ya ci wa Liverpool kwallaye 28 a bara, rabonsa da ya taka leda tun cikin watan Agustan da ya wuce.