Cristiano Ronaldo ya yi ganganci

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Real Madrid har yanzu tana matsayi na daya a teburin La Liga

Cristiano Ronaldo, ya yi wauta a gasar La Liga ranar Asabar, bayan da ya yi wa dan wasa keta, sannan ya yi mari da naushi da sauran laifuka da ya aikata a wasan.

An bai wa dan kwallon Real Madrid, mai shekaru 29, jan kati saura minti bakwai a tashi daga wasan, sakamakon ketar da ya yi wa Edimar.

Tun farko Ronaldo ya fara naushin mai tsaron baya Jose Angel Crespo, amma alkalin wasa bai gani ba, sai kuma ya yi wa Edibar keta ta baya sannan ya shararawa dan wasan mari.

Wata kila a yankewa Ronaldo hukuncin hana shi buga wasanni uku, wanda zai iya fara aiki a lokacin da za su kara da Atletico Madrid ranar 7 ga watan Fabrairu.

Real Madrid ce ta doke Cordoba da ci 2-1 har gida, kuma Ghilas ne ya fara cin Madrid a bugun fenariti, kafin Benzema ya farke, sannan Bale ya kara ta biyu a bugun fenariti.