Tunisia da Jam. Congo sun kai wasan gaba

Tunisia Congo DR Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a fara buga wasannin daf da na kusa da karshe ranar Asabar

Tunisia ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar kofin Afirka, duk da tashi kunnen doki da suka yi da Jamhuriyar Congo.

Tunisia ce ta fara zura kwallo ta hannun Ahmed Akaici, sannan Jamhuriyar Congo ta farke kwallonta ta hannun Bokila a minti na 66.

Haka kuma Tunisia ce ta jagoranci rukuni na biyu da maki biyar, sai Jamhuriyar Congo a mataki na biyu da maki uku, Cape Verde ma da maki uku sai Zambia ta karshe da maki daya.

Za a buga wasan daf da na kusa da karshe ranar Asabar tsakanin Congo da Jamhuriyar Congo sai kuma karawa tsakanin Tunisia da Equatorial Guinea.