Australia Open: Venus ta kai wasan 'yan 8

Venus Williams Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Idan ta samu nasara za ta kara da Serena a wasan daf da na karshe

Venus Williams ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar Tenis ta Australia Open, bayan da ta doke Agnieszka Radwanska.

Venus ta kai wannan matsayin ne bayan da ta casa Radwanska da ci 6-3 da 2-6 da kuma 6-1.

Kuma wannan ne karon farko da 'yar wasan ta kai wannan matsayin tun a shekarar 2010.

Haka kuma za ta kara da Madison Keys a wasan daf da na kusa da karshe, idan ta samu nasara ta fafata da Serena a wasan daf da na kusa da karshe.

Serene ta kai wasan daf da na kusa da karshe ne bayan da ta doke Garbine Muguruza da ci 2-6 da 6-3 da kuma 6-2.