Ba za mu sayar da Balotelli ba – Rodgers

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Rodgers ya ce Balotelli dan wasa ne na gari

Kociyan Liverpool Brendan Rodgers ya ce ba za su sayar da dan wasa Mario Balotelli a lokacin musayar 'yan kwallo da ake yi a wannan wata na Janairu ba.

Rodgers ya ce zai bai wa dan wasan kowacce dama domin ya dawo ganiyarsa a kulob din.

Ba a sanya Balotelli a wasan da kulob din ya buga ba a zagaye na hudu na Gasar cin Kofin Ingila inda suka yi kunnen doki da Bolton.

Hakan ya sa ana ta rade radin cewa dan wasan -- mai shekaru 24 -- ba zai sake yin tagomashi a Anfield ba.

Sai dai ranar Litinin Rodgers ya ce "batun ba haka yake ba. Lokaci ne da dan wasan ke fuskantar kalubale amma shi dan wasa ne na gari."