Real Madrid ta dauko Lucas Silva

Lucas Silver Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid tana matsayi na daya a teburin La Liga

Kungiyar Real Madrid ta dauko dan wasan Brazil, Lucas Silva daga Cruzeiro kan kwantiragi mai tsawon, akan kudi sama da fam miliyan 9.

Dan wasan, maishekaru 21, hannu akan yarjejeniyar taka leda a Madrid har zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2020.

Silva yana cikin tawagar 'yan wasan Brazil 'yan kasa da shekaru 21, sannan ya taimaka wa kungiyarsa lashe kofin Brazil a shekarar 2013 da kuma 2014.

A cikin makonnan Real Madrid ta dauko Martin Odegaard, mai buga wasan tsakiya mai shekaru 16 da haihuwa.