Mulumbu ba zai buga wasan da za su yi da Congo ba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mulumbu yana fatan komawa taka leda nan ba da dadewa ba

Kyafin din DR Congo, Youssouf Mulumbu, ba zai yi wasan dab da na kusa da na karshe da kasarsa za ta fafata da Congo ranar Asabar ba.

Dan wasan, mai shekaru 28, bai buga wasan da suka yi kunnen-doki da Tunisia ranar Litinin ba saboda ciwon da ya ji a kafadarsa, kuma ana tsammani zai ci gaba da zama a benchi.

Dan wasan tsakiyar na West Brom ya ce "likitoci na yin bakin kokarinsu domin tabbatar da cewa na koma taka leda. Ina da tabbacin cewa abokan aiki na za su yi kokarin ganin mun kai matakin kusa da na karshe.

Youssouf Mulumbu ya ji rauni ne lokacin fafatawar da suka yi da Cape Verde.