Samuel Eto'o ya koma Sampdoria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samuel Eto'o ya koma Sampdoria

Dan wasan kulob din Everton, Samuel Eto'o ya rattaba hannu kan kwantaraginsa da kungiyar wasa ta Sampdoria har zuwa 2018.

Eto'o ya je Everton a watan Agustan 2014, bisa tsarin musayar 'yan wasa.

Ya kuma samu nasarar cin kwallaye hudu a wasanni 20 da ya buga wa kulob din.

Kociyan na Everton, Roberto Martinez ya ce" a madadin kungiyar Everton, muna yi masa fatan alkairi dangane da sabon kulob din da zai koma".