FIFA: An kashe $4bn a kan musayar 'yan wasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption FIFA ta ce Ingila ce ta fi kashe kudi wajen musayar 'yan kwallo a bara.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta ce kulob-kulob sun kashe kimanin $4.1bn wajen yin musayar 'yan kwallo a bara.

Hukumar ta ce Ingila ce kasar da ta fi kashe kudi wajen musayar 'yan kwallo, domin kuwa kulob-kulob din ta sun kashe $1.2bn a shekarar 2014.

A cewar hukumar, kulob-kulob na Spaniya su ne na biyu, domin kuwa sun kashe $700m a musayar 'yan wasan.

Fifa ta ce India ce kasar da ta sayi dan wasan da ya fi tsufa a shekarar 2014, yayin da a karon farko, China ta shiga jerin kasashe goma da suka fi kashe kudi domin sayen 'yan wasa a duniya.

Fifa ta ce lissafinta bai hada da musayar 'yan kwallon da aka yi tsakanin kulob-kulob da ke cikin kasa daya ba.