Ghana ba ta tsoron kowace kasa - Asamoah

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Blac Stars, Asamoah Gyan,

Kyaftin din kungiyar kwallon kafar Black Stars ta kasar ya ce ba sa tsoron kara wa da kowacce kasa, a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Ya ce "bisa dogaro da karfin da kungiyarmu take da shi, za mu iya tunkarar kowa a wannan gasar".

Gyan ne dai ya zura kwallaye biyu a ragar Afirka ta Kudu abin da ya sanya Ghana ta samu cancantar zuwa wasan dab-da-na-kusa-da-na-karshe.

Kungiyar Black Stars dai za ta kara da kasa ta biyu a rukunin D a wasan dab-da-na-kusa-da-na-karshe, ranar Lahadi.