An ci tarar Mourinho £25,000.

Image caption An gargadi Mourinho da kada ya sake yin irin wannan zargi.

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ci tarar kociyan Chelsea, Jose Mourinho, pan £25,000 saboda zargin da ya yi cewa alkalan wasa na yi wa kulob din makarkashiya.

Mourinho ya yi zargin ne bayan alkalin wasa ya ki bai wa Chelsea bugun fenareti a wasan da suka tashi 1-1 da Southampton ranar 28 ga watan Disamba.

Hukumar ta bayyana zargin da cewa "bai dace ba kuma kalamin nasa ya yi illa ga kimar wasan".

Hukumar ta gargade shi da kada ya sake yin irin wannan zargi, koda yake ta wanke shi daga tuhumar da aka yi masa cewa ya zargi alkalin wasa da nuna son kai.