Arsenal ta sayi Paulista a kan £11m

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Paulista ya ce ya dade yana son buga wasa a kulob din Turai.

Kulob din Arsenal ya sayi dan wasan baya na Villarreal Gabriel Paulista a kan kudi £11.2m.

Dan wasan dan kasar Brazilian, mai shekaru 24, ya taka leda sosai a Villarreal kuma ana sa rai zai buga wasan da za su yi da Aston Villa ranar Lahadi.

Gabriel ya ce: "Na tattauna da iyali na, inda na shaida musu cewa buri na shi ne na taka leda a kulob-kulob na Turai."

Ya yi kira ga magoya bayansa su saurari irin bajintar da zai nuna idan ya koma Arsenal.