FA ta dakatar da Costa daga buga wasanni uku

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Costa ya musanta zargin

Hukumar kwallon kafar Ingila ta dakatar da dan wasan Chelsea Diego Costa daga buga wasanni uku.

Hukumar ta ce ta dauki wannan mataki ne bayan ta same shi da laifin taka dan wasan Liverpool, Emre Can.

Dan wasan, mai shekaru 26, ba zai buga wasannin da kulob din zai yi da Manchester City da Aston Villa da kuma Everton na gasar Premier ba.

Costa dai ya musanta cewa ya taka Emre a wasan kusa da na karshe na cin kofin League da suka yi ranar Talata.

Costa, wanda kulob din Chelsea ya saya a kan £32m, ya zura kwallaye 17 a wasanni 19 da ya buga a gasar Premier a kakar wasa ta bana.