Liverpool za ta sayi Danny Ings

Image caption Danny Ings zai ci gaba da koma Liverpool a karshen kakar wasanni.

Kulob din Liverpool yana son sayen dan wasan Burnley, Danny Ings sai dai zai bar shi a kulob din a matsayin aro har karshen kakar wasa ta bana.

A baya dai kulob din Tottenham da Real Sociedad sun nuna sha'awar sayen dan wasan, wanda zai kammala wa'adinsa a Burnley a watanni shida masu zuwa.

Sai dai kulob din Burnley yana so dan wasan ya ci gaba da taka masa leda zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Liverpool zai biya kudin sayen dan wasan duk da yake ba zai buga musu wasa ba sai karshen kaka wasanni, kasancewarsa dan shekaru 24.

Danny Ings ya koma Burnley ne daga Bournemouth a watan Agustan shekarar 2011 a kan kudi kusan £1m.

Ya zura kwallaye bakwai a gasar Premier Leaguea a kakar wasa ta bana.