Jerome ya janye daga takarar FIFA

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jerome ya yi zargin cewa wasu ne ke son kawar da shi

Jerome Champagne ya janye daga yin takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya bayan ya kasa samun goyon bayan hukumomin kwallon kafa da yawa.

Bafaranshen -- wanda ke bukatar goyon baya daga akalla hukumomin kwallon kafa guda biyar -- ya ce ya samu goyon bayan hukumomin kwallon kafa uku ne kawai a yunkurinsa na maye gurbin shugaban FIFA, Sepp Blatter.

A wata sanarwa da ya fitar, Jerome ya ce "Ina matukar bakin cikin shaida muku cewa ban samu amincewar hukumomin kwallon kafa guda biyar ba, wadanda nake bukata domin zama dan takara ."

Za a gudanar da zaben shugabancin hukumar ne ranar Juma'a, 29 ga watan Mayu.

Jerome, mai shekaru 56 a duniya, wanda kuma tsohon jami'in Fifa da na jakadanci ne, ya yi zargin cewa "wasu ne daga cikin hukumar" ke yunkurin kawar da shi.