Kulob din Man Utd ya sayi Andy Kellett

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kellett zai koma Manchester United ne a matsayin aro

Kulob din Manchester United ya sayi dan wasan baya na Bolton, Andy Kellett, a matsayin aro zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Hakan na faruwa ne a yayin da shi kuma dan wasan Manchester United, Saidy Janko, zai koma Bolton din a matsayin aro zuwa karshen kakar wasan.

Sau hudu kawai Kellett, mai shekaru 21 a duniya, ya taka leda a rukinin manyan 'yan wasa na Bolton, kuma ya kwashe watanni uku a rukunin League Two na kulob din Plymouth Argyle a matsayin aro tun daga farkon kakar wasanni ta bana.

Shi kuwa dan wasan na tsakiya, Janko, mai shekaru 19, har yanzu bai taka leda a rukunin manya na United ba.

A makon jiya ne dan wasan baya, Sadiq El Fitouri, ya koma United daga Evo-Stik.