Za a sayar da Ronaldo a kan £300m

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ronaldo ya doke Messi, inda ya lashe gasar Gwarzon dan kwallon kafa a bana.

Wakilin Cristiano Ronaldo ya ce kudin da za a sayi dan wasan zai kai £300m idan kulob din Real Madrid ya yanke shawarar sayar da shi.

Jorge Mendes ya shaida wa BBC cewa Ronaldo "shi ne dan wasan da ba a taba samun irinsa a tarihi ba" kuma yana da basira ta musamman.

Mendes ya kara da cewa, "idan har wani dalili zai sa kulob din Real Madrid ya sayar da shi [Ronaldo], to duk wanda zai saye shi zai biya £300m."

Ronaldo, mai shekaru 29 a duniya, shi ne ya lashe Gasar Gwarzon dan kwallon kafa a watan jiya, karo na biyu a jere, inda ya doke Lionel Messi.