Diafra Sakho: Fifa na iya korar West Ham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sakho ya taka leda a West Ham kwanaki kadan bayan ya ce ba shi da lafiya.

Kulob din West Ham zai iya fuskantar kora daga gasar cin kofin Ingila idan Fifa ta gano cewa ya karya doka kan zaben dan wasa, Diafra Sakho.

Sakho, mai shekaru 25, ya janye daga bugawa kasarsa ta Senegal a gasar cin Kofin nahiyar Africa saboda ciwon bayan da yake fama da shi.

Sai dai kwanaki 18 bayan ya ce yana ciwon baya, ya taka leda a West Ham, har ma ya zura kwallo a fafatawar da kulob din ya doke Bristol City 1-0 a Gasar cin Kofin Ingila.

Dokar Fifa ta bayyana cewa dan wasa ba zai bugawa kulob din sa kwallo ba idan dai kasarsa ta bukace shi domin ya taka mata leda.

Yanzu haka dai Fifa ta fara gudanar da bincike kan batun, koda yake kulob din na West Ham ya musanta cewa ya karya doka.