Redknapp ya yi murabus daga QPR

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Redknapp ya ce bai kamata ya ci gaba da zama a matsayin kociya ba

Harry Redknapp ya sauka daga mukaminsa na kociyan kulob din QPR, yana mai cewa ya yi hakan ne saboda tiyatar da za a yi masa a gwiwa.

Kociyan, mai shekaru 67, ya shaida wa shugaban kulob dinTony Fernandes matsayinsa na son barin kulob din wanda ke na biyun karshe a tebirin Gasar Premier.

Redknapp ya ce, "Ina bukatar a yi min tiyata da gaggawa. Idan dai hakan zai sa ba zan yi himma dari bisa dari ba, bai kamata na ci gaba da kasancewa kociya ba."

Jami'an kulob din guda biyu: Les Ferdinand da Chris Ramsey ne za su shugabanci kulob din a matsayin rikon-kwarya.