Wane tsawon lokaci zai dauke ka kafin ka samu albashin babban dan kwallo?

Wane tsawon lokaci zai dauke ka kafin ka samu albashin babban dan kwallo?

Manyan ‘yan kwallo a duniya na karbar albashi mafi tsoka a duniya.

Cristiano Ronaldo a kwangilarsa tare da Real Madrid na karbar kusan Euro €350,000 ko £265,000 a kowanne mako.

Wane tsawon lokaci zai dauke ka kafin ka karbi albashin babban dan kwallo?

Ka yi amfani da na’urar lissafi watau kwakuleta domin gano na ka - wannan tsari na cikin shirin BBC na duniyar da arzikinta ya karu.

Nau’rar lissafi ko kwakuleta

Masu kungiyoyin kwallon kafa a Turai sun kashe makudan kudade a watan Junairu domin sayen manyan ‘yan kwallo a kasuwar musayar ‘yan kwallo.

A jumlace, kungiyoyin kwallo 20 na gasar Premier sun kashe fan miliyan 950 a kakar wasa ta bana, kuma manyan ‘yan wasa na kara samun karin kudade na mako-mako fiye da yadda suke samu a baya.

A shekarar 2001, lokacin da Sol Campbell ya bar Tottenham ya koma Arsenal, ana ba shi fan 100,000 a kowanne mako, abin da ya sa ya zama dan kwallon Birtaniyar da yafi kowanne karbar albashi.

Bayan shekaru 14, Wayne Rooney ya sabunta kwangilarsa a Manchester United inda ya soma karbar fan 300,000 a kowanne mako.

Kamar yadda mujallar Deloitte wacce ta kware a harkar kudaden kwallon kafa ta bayyana, akalla ‘yan wasan Premier na karbar fan miliyan 1.6 a kakar wasa ta 2012 zuwa 2013. Watau fan 31,000 a kowanne mako abin da ya zartar matsakaicin albashin ma’aikata a Biritaniya a duk shekara.