AFCON: Ghana ta soki E. Guinea

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption An jefi 'yan wasa da magoya bayan Ghana

Jami'an hukumar kwallon kafar Ghana sun yi suka kan rikicin da ya barke a filin wasan Malabo lokacin da kasar ta doke Equatorial Guinea 3-0 a Gasar cin Kofin nahiyar Africa.

Magoya bayan Equatorial Guinea dai sun yi ta jifan magoya bayan Ghana, lamarin da ya sa aka dakatar da wasan tsawon mintuna talatin.

Shugaban hukumar kwallon kafar Ghana Kwesi Nyantakyi ya bayyana lamarin da cewa "dabbanci ne da ya kai kololuwa".

Ya kara da cewa abin da ya faru ya yi matukart bata musu rai, koda yake ya kara da cewa ya godewa Allah tunda babu wanda aka kashe.

Ghana dai za ta fafata Ivory Coast a wasan karshe bayan lallasawar da ta yi wa Equatorial Guinea a wasan kusa da na karshe.