Ivory Coast ta lashe Kofin Africa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ivory Coast ta doke Ghana 9-8 a bugun fenareti

Ivory Coast ta doke Ghana a Gasar cin Kofin nahiyar Africa, kuma ta lashe kofin.

Hakan ya faru ne bayan bugun fenaretin da kasashen suka yi sakamakon rashin nasarar kowacce daga cikinsu.

A bugun fenaretin, golan Ivory Coast Boubacar Barry ya doke kwallon da Ivory Coast ta buga, kana ya zura kwallon da aka ba shi, lamarin da ya sa suka tashin da ci 9-8.

Wannan shi ne karo biyu da Ivory Coast ta doke Ghana, kana ta lashe kofin tun shekarar 1992.

A shekarar ta 1992, Ivory Coast ta doke Ghana da ci 11-10 a bugun fenareti.